ABNA24 : Bayanai sun ce taron ya samu halartar bangarori daban daban, duk da cewa dai akwai wasu da basu halarci taron ba.
Gamayar kungiyoyin tsaffin ‘yan tawayen yankin Azawad na daga cikin wadanda basu halarci taron ba.
Bangarorin da sukayi boren ganin shugaban kasar ya yi murabus sun halarci taron, koda yake sun koka akan rashin samun wakilci mai yawa a taron.
Shehun malamin nan Imam Dicko da tsohon firaministan kasar Modibo Sidibé, na daga cikin mahalarta taron, saidai Choguel Maïga wanda wani jigo ne a bangarorin da sukayi zanga zanga a kasar na M5 bai halarci taron, wanda ake bayyana shin a manuniya ce ta rashin jituwa tsakanin sojojin da kuma bangarorin da sukayi boren kin jinin tsohon shugaban kasar.
342/